6 Janairu 2022 - 15:58
​Mai Shiga Tsakani Na ECOWAS Na Ziyara A Mali

Tsohon shugaban tarayyar Najeriya, Goodluck Jonathan, kana mai shiga Tsakani kan rikicin Mali na kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, ya isa birnin Bamako game da jadawalin da sojoji suka gabatar na yin mulkin rikon kwarya na Karin tsawon shekaru 5.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Babu dai wani Karin bayyani da akayi amma an ce Mista Jonatan, na dauke da sako daga shugaban kasar Ghana kan shugaban kungiyar ECOWAS, Nana Akufo-Ado.

Ziyarar kuma wani bangare na shirin taron gaggawa shugabannin da gwamnatocin kungiyar da za’a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa.

Wakilin na ECOWAS zai kuma gana da shugaban rikon kwaryar soji na Malin Kanal Assimi Goita da kuma wakilai da jakadun kasashe ketare

A halin da ake ciki dai shugabannin kasashen yankin da dama sun bayyana rashin gamsuwarsu da shirin sojojin na tsawaita wa’adin mulki, a wani mataki da sojojin na Mali suka ce na samun sukunin shirya zabubuka ne.

Ko baya ga hakan jam’iyyun siyasa da bangarori daban daban na Mali, sun yi watsi da jadawalin zaben da sojoji suka fitar wanda suka ce tamakar tsawaita juyin mulki ne.

342/